NAF: An murkushe wasu yan bindiga a Katsina …

HASSAN TURAKI.

Dakarun Sojin Saman Najeriya (NAF), sun kashe manyan shugabannin ’yan bindiga guda biyu, Gero (Alhaji) da Alhaji Riga, tare da wasu mayaƙansu sama da 20 a wani hari ta sama da suka kai a Jihar Katsina.

Harin ya faru ne a ranar Laraba, 13 ga watan Maris, a dajin da ke Ƙaramar Hukumar Faskari.

Rundunar Operation Fansan Yamma ta NAF ce ta ƙaddamar da harin bayan samun sahihan bayanai kan maɓoyar maharan.

A cewar Mataimakin Kakakin NAF, Kyaftin Kabiru Ali, dakarun sun lalata sansanin maharan tare da kashe ƙarin ‘yan ta’adda a tsaunukan da ke kusa, kuma har yanzu ana ci gaba da binciken irin ɓarnar da aka yi musu.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *