HASSAN TURAKI.
Sakamakon binciken kwakwaf da bin diddigi gami da sumame irin na yan sanda, sunyi nasarar ganowa tare da cafke malamin da ake zargi da kashe dalibin sa kuma ya cire masa kai da al’aurar sa.
Kamar yadda kakakin rundunar yan sandan jihar Jigawa SP Lawan Shi’isu Adam ya shaida wa manema labarai cewa hukumar tayi nasarar kama Mal. Musa Wada me shekaru 45 dan asalin garin Jikas-Dabaja ta karamar hukumar gwaram da zargin kashe almajirin sa me suna Bashir Adamu kuma ya cire masa kai da al’aurar sa.
Yayin gudanar da bincike a sashin bincike na babbar ofishin hukumar yan sanda, tuni dai malam Musa Wada ya tabbatar da cewa shine ya kashe almajirin sa Bashi Musa kuma ya cire masa kai da al’aurar sa.
Ya kara da cewa ya kama almajirin sa Bashir ne da laifin rashin zuwa makaranta kuma ya gaza bada hujja, yayin da yake masa hukunci ya fita hayyacin sa harma rai yayi halin sa.
Musa ya kara da cewa ya cire masa kai da al’aurar sa ne saboda ace matsafa ne suka kashe shi. Malamin ya shaida wa yan sanda yayin bincike cewa; ya bunne kan almajirin da kuma al’aurar sa a gonar sa.
Idan ba’a manta ba, GuaranteeNews ta labarta muku cewa ranar 12/3/2025 an tsinci gawar almajiri me suna Bashir Adamu a gefen hanya a kauyen Jikas-dabaja an yanke masa kai dama al’aurar sa, daga baya an gano cewa almajirin malam Musa Wada ne, bayan kammala bincike aka mika gawan sa wa iyayen sa sukayi masa sutura.
Yanzu haka dai Musa Wada wanda tuni ya amsa laifin sa, yana hanun yan sanda sashin bincike kuma za’a gurfanar da shi a gaban kuliya manta sabo domin girbe abinda ya shuka.
ALLAH ka tsare mu da aikin dana sani.
Leave a Reply