JIGAWA: Anyi wa amarya yankan rago a Hadejia …

Hassan Turaki.

Hukumar yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da labarin rasuwar wata amarya da aka kashe ta me suna Zainab Ibrahim yar shekara ashirin da biyu (22) a unguwar warware dake karamar hukumar Hadejia ta jihar Jigawa sati biyar (5) da auren ta.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar SP Lawan Shi’isu Adam ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace bayan samun labarin ne hukumar yanda na Hadejia sukayi dirar mikiya a gidan kuma suka riske ta cikin jini da mummunan yanka a makogoron ta, sun yi hanzarin garzaya wa da ita babban asibitin Hadejia inda kwararren likiti ya tabbatar da rasuwar amaryar me sati biyar kacal da aure.

Tuni dai hukumar yan sanda ta baza kamar ta domin aiwatar da binciken gano wadan da suka aikata wannan ta’asa gami da iza keyar su zuwa gaban kuliya domin karbar hukunci daidai da abinda suka aikata.

ALLAH ya kyauta.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *