Gwamatin Tarayya Za ta kammala Aikin Madatsar Ruwa Ta Dasin Hausa …

Hassan Turaki.

Gwamnatin Shugaba Tinubu ta shirya gaggauta kammala aikin madatsar ruwa ta Dasin Hausa da ke jihar Adamawa. Aikin wanda aka dakatar tun a shekarun 1980s zai magance ambaliyar ruwan da ke fitowa daga madatsar ruwa ta Lagdo a Kamaru.

Rahotanni sun bayyana cewa ma’aikatar albarkatun ruwa da hukumar ICRC da gwamati za su haɗa gwiwa da kamfanin Mainstream Energy domin gaggauta aikin, a karkashin tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP).

Idan aka kammala Madatsar ruwan ta Dasin Hausa, za ta samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 300, kana ta bayar da damar noman rani a gonakin da suka kai hekta 150,000 a jihohin Adamawa, Taraba da Benuwai, tare da kare dukiyoyin da kimarsu ta kai biliyoyin Nairori daga ambaliya a duk shekara.

Baya da kare ambaliya da samar da wutar lantarki da noma, ana sa ran kammala madatsar zai farfaɗo da tattalin arziki da ƙarfafa gwiwar al’ummomin da ke yankin na kogin Taraba, Adamawa, Neja da Benuwai


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *