NCC: Za’a kulle wasu shafukan yanar gizo bisa umarnin majalissar tarayya

Hassan Turaki.

Majalisar Wakilan Najeriya ta bai wa Hukumar Sadarwa ta NCC umarnin rufe duk wasu shafukan yanar gizo masu nuna batsa a Najeriya.

Majalisar ta ba da wannan umarnin ne yayin zaman ta na ranar Talata, inda ta nemi hukumar sadarwar ta umarci duk kamfanonin da ke samar da intanet su rufe duk wasu shafukan intanet da ke nuna hotuna ko bidiyon batsa cikin gaggawa.

Wannan umarni na zuwa ne bayan wani ƙudiri da ɗan majalisa daga Jihar Katsina, Dalhatu Shehu Tafoki, ya gabatar.

Tafoki ya bayyana cewa bidiyoyin batsa da ke intanet na zama babbar matsala a duniya, kuma zuwa yanzu Najeriya ba ta ɗauki wani matakin magance matsalar ba.

Ya kafa hujjar cewa Najeriya ƙasa ce mai addini, inda manyan addinan ƙasar suka haramta batsa da kuma nuna tsiraici.

Tafoki ya kuma bayyana gargaɗin da masana halayyar ɗan Adam suka yi kan mummunan tasirin da kallon bidiyon batsa ke da shi, ciki har da yiwuwar kusantar zina, da karuwanci, da kuma kasa rabuwa da kallon.

Majalisar ta kuma buƙaci hukumar NCC ta hukunta duk kamfanin samar da intanet da ya bijirewa wannan umarnin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *