TALLAFI: Gidauniya ta sauke kabakin arziki a taura …

Hassan Turaki.

A yau kungiyar baitul abla ta sake dawowa Taura domin rabon tallafi ga al’ummar da suke kusa da wajen da zasu gina makarantar koyon sana’a dake Tsamiyar kabau.

Shugabar baitul abla a nigeria hajiya fatima tayi rabon shinkafa sama da buhu (100) da sauran kayayyakin sawa dana wasan yara ga fulanin wannnan gari.

A nasa bangaren shugaban karamar hukumar taura Hon shuaibu Hambali ya karbi bakin tare da nuna godiyar sa ga wannan gagarumin aiki na sama da miliyan dari hudu da wannan kungiya zata yiwa wannan gari.

A jawabin godiya shugaban kungiyar TAURA FOUNDATION MALAM IBRAHIM KAMAL a madadin kungiyar Taura foundation wanda itace ta jagoranci al’amuran wannan kungiya ta sun sake godiya bisa yadda baitul abla ta kawo wannan babban alkairi wannan gari.

A shekarar nan ake saka ran fara aiwatar da ginin wannan waje wanda zai kunshi Masallaci da Makaranta.

Tace wannan ba karamin cigaba aka samu a yankin ba, domin matasan zasu koyi abubuwa da dama wanda har daukar nauyi zasu yi zuwa kasar waje.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *