SERAP: ku janye dawo da Natasha ko mu haɗu a kotu – inji serap

Hassan Turaki.
Ƙungiyar SERAP, mai fafutukar haƙƙin ɗan Adam da yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya gaggauta janye dakatarwar da majalisar ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
SERAP ta ce dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha ba komai ba ne illa tauye mata ’yancinta na faɗin alabarkacin baki, wanda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba ta.
Cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta fitar a ranar 8 ga watan Maris, SERAP tace muddin ba a kiyaye wannan gargaɗi ba za ta ɗauki matakin shari’a nan da sa’o’i 48.
Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun matamaikin shugabanta, Kolawole Oluwadare, SERAP ta ce kasancewar Natasha a matsayin Sanata ba zai haramta mata ’yancinta na faɗin albarkacin baki ba.
SERAP ta nanata cewa dakatar da Sanata Natasha ya saɓa wa duk wasu tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya da kuma Dokokin Duniya da suka sahale mata ’yanci a matsayinta na bil Adama.