Hassan Turaki.
Shugaban Asibitin Tarayya dake Birnin Kudu (FMC) Dr. Adamu Abdullahi Atterwahmie na farin cikin sanar da daukacin al’ummar Jihar Jigawa da kewaye cewa Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta hannun Babban Ministan Lafiya Dr. Muhammad Ali Pate, ta ƙaddamar da muhimman shirye-shirye guda biyu domin inganta kiwon lafiya da ceton rayuka a faɗin ƙasar nan.
- Shirin CEmONC (Comprehensive Emergency Obstetric Care)
Wannan shiri an ƙirƙire shi ne domin haɓaka kiwon lafiyar mata masu juna biyu da jarirai, tare da tabbatar da cewa asibitoci da cibiyoyin lafiya suna da kayan aiki da ƙwararrun ma’aikata domin magance matsalolin da suka shafi haihuwa da bayan haihuwa. Wannan shiri zai bayar da:
-Yin tiyatar haihuwa (C-section) ga mata da ke cikin wahalar haihuwa kyauta
- Karin Jini ga marasa lafiya domin magance matsalar zubar jini mai yawa
- Magance matsalolin ciki kamar ciwon eclampsia (Jijjiga), zubar da jini, da kuma haihuwar da ta tsaya
- Shirin NEMSAS
Wannan shiri zai tabbatar da cewa dukkan ciwo na gaggawa - Shirin NEMSAS Wato National Emergency Medical System and Ambulance Service.
Wannan shiri zai tabbatar da cewa dukkan dan Nigeria da ya samu ciwo na gaggawa, ko yake bukatar kulawa ta gaggawa, ya samu wannan kulawa cikin lokacin da yake bukata KYAUTA. Marar lafiya zai iya zuwa asibitin FMC Birnin Kudu da kansa, ko a kawo shi, ko ma idan babu wannan damar, zai iya kiran Lambourn wayar da za a bayar, Ambulance daga asibitin za ta zo ta dauke shi kyauta ta kawo shi asibitin. Dukkan kulawa da za a bashi a cikin kwana biyu na farko KYAUTA NE.
Leave a Reply