KANO: An kama wasu da suka zo Kano sayan bindiga …

Ibrahim A makama.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa shiya sanar da hakan, inda yace an kama wadanda ake zargin Yan ta’adda ne da suka hadar da: Shukurana Salihu da Rabi’u Dahiru sai Ya’u Idris dukkanin su yan asalin Jihar Katsina, na karshen su shine Muktar Sani dake Unguwar Yandodo a Hotoron Jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa sun zo Kano ne dan siyan Bindiga kirar AK-47, da isowar su wannan Jihar, Yan Sanda suka cika hannu dasu a yankin Hotoro Yandodo.

An kama su da wasu Kananan Bindigogi da harsashai dai guraye da Layu da addina harma da kudade sama da Naira Miliyan 1.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *