GARKI: An yaba wa karamar hukumar Garki …

Hassan Turaki.

Shugaban karamar Hukumar garki Hon Adamu Hudu Kore Jarman Garki tare da baban siyasa Hon. Muhammad Lawan Garba Bullet sun kai ziyarar aiki irin na gani da ido a karamar hukumar Garki domin gane wa mai girma gwamna yadda Al’uma ke amfanar shirin noman rani a yankin karkara dake karamar hukumar.

Yayin wannan ziyara, shugaban karamar Hukumar ta Garki ya kuduri Aniyar Farfado da noman rani A karamar Hukumar garki domin fadada harkokin noman rani don ciyar da al’umar karkara gaba ta fannin tsarin tallafin gwamnatin karamar hukuma da ta jiha karkashin jagorancin Mal. Umar A. Namadi.

A nasa bangaren Hon. Muhammad lawan bullet ya yaba da kokarin shugabancin karamar hukumar harma ya sha alwashin shaida wa gwamna duk abubuwan da ya gane wa idon sa. Ya kara da cewa shugabancin karamar hukumar Garki karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar Hon. Adamu hudu kore ya taka muhimmiyar rawa wajen fadada harkar noma irin na zamani a yankin karamar hukumar.

Anas Abdulwahab sayori,

S.A Media Garki LGA,

8-3-2025.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *