BAUCHI: Sabuwar cibiyar cinikayya ta fitar da sanarwa …

Hassan Turaki.

Sabuwar Cibiyar Cinikayya ta jihar Bauchi tareda hadin gwiwar kwamitin kula da cibiyoyin cinikayya ta kasa suna gayyatar kungiyoyin ‘yan kasuwa da masana’antu irinsu: Bauchi Chambers of Commarce, Manufacturers Association of Nigeria, Nigerian Association of Small and Medium Enterprises (NASME), National Association of Small Scales Industrialist (NASSI), da Market Tradeas Association of Nigeria (MATAN), da dukkanin kungiyoyin ‘yan kasuwar jihar Bauchi.

Kazalika ana gayyatar Bankuna da duk ma’aikatatun jiha da na tarayya da su ka shafi harkar kasuwanci, da su halarci taron gangamin wayar da kai game da tsarin aiwatar da yarjejeniya ta kasa da kasa kan harkar kasuwanci, karkashin cibiyar kasuwanci ta duniya da kuma tsarin aiwatar da yarjejeniyar kasuwanci ta kasa da kasa ta nahiyar Afirka.

Za’a yi wannan taro ne, a babban dakin taron Command Guest House Bauchi, ranar Litinin 10 ga watan Maris, 2025, da karfe 09:00 na safe.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *