Saleh Umar Andaza.
Lina Medina ƴar asalin ƙasar Peru itace uwa mafi ƙanƙantar shekaru a tarihi.
Lina Medina ta haihu tana da shekaru biyar da wata 7 da kwanaki 17 a duniya a wani asibiti dake babban birnin ƙasar wato Lima a hannun wani likita mai suna Dr. Gerardo Lodazo a ranar 14 ga watan Mayu, 1937, inda ta haifi ɗa namiji mai nauyin kilogram 2.7 aka saka masa suna Gerardo.
Gerardo da farko ya ɗauka Lina Medina ƴar uwarsa ce sai daga baya a loƙacin yana ɗan sheƙara goma a duniya ya gane mahaifiyar sa ce. Sannan Gerardo ya rayu a duniya har tsawon shekaru 40.
Leave a Reply