Isyaka I. Wunti.
Gidauniya Ta Ba Da Tallafin Shinkafa Ga Al’ummar Musulmi A Kananan Hukumomi 20 na Jihar Bauchi.
Wata kungiyar agaji da ke Bauchi mai suna ‘Wunti Al-khair Foundation’ ta kaddamar da rabon shinkafa ga al’ummar Musulmi marasa galihu da ke fadin kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi.
An gudanar da fara rabon tallafin ne daga kananan hukumomin Katagum, Zaki, Gamawa da Giade.
A kalla marasa galihu 250 zasu amfana da wannan tallafin a kowace karamar hukuma 20, da sauran kingiyoyin mabukata aka zabo inji Manajan shirye-shirye na kungiyar Mustapha Ango.
Ya bayyana cewa an yi shirin ne domin kawo agajin da ake bukata ga marasa galihu, musamman a wannan wata na azumin Ramadan.
Shi ma da yake nasa jawabin, wani jami’in gidauniyar Isiyaka Wunti, ya ce baya ga rabon kayan abinci na watan Ramadan, gidauniyar Wunti Al-khair tana gudanar da ayyukan jin kai daban-daban da suka hada da bayar da magani kyauta da kuma tallafin karatu ga marasa galihu.
Wadanda suka ci gajiyar shirin sun nuna jin dadinsu ga gidauniyar.
Leave a Reply