ZAMFARA: Mutum 12 sun rasa ransu yayin arangama da yan ta’adda …

Barayin daji dauke da muggan makamai sunyi garkuwa da mutanen dake hakar zinari a hanyar malamawa zuwa adabka dake karamar hukumar Bukkuyum ta jihar zamfara.

A lokacin da yan sakan yankin na Adabka suka samu labarin abunda ke faruwa sunyi gangami sukabi bayan barayin domin kubuto da wadan da barayin suka dauka yayin da barayin dajin sukayi wa yan sakan kwanton bauna suka kashe mutane goma sha biyu suka jikkata mutum tara.

Ganau ya sheda wa nahiyar mu cewa daga cikin wadan da aka kashe a lokacin artabun akwai mutum ukku daga garin Adabka, sai mutum biyar daga kauyen sabuwar tunga, mutum daya daga ganar kiyawa, mutum daya daga kuka duke, mutum daya daga dogon dajin mai baka sai daya daga gandun malam.

Muna adduar Allah yajikansu da rahama wadanda sukaji raunukka Allah yabasu lafiya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *