Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel kan zargin almundanar naira biliyan 700.
EFCC ta tsare tsohon gwamnan ne bayan ya amsa gayyatar ta a ranar Talata domin amsa wasu tambayoyi kan zargin karkatar da kuɗi da wata ƙungiya mai rajin yaƙi da masu zamba ta yi masa.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa tsohon gwamnan ya karɓi naira tiriliyan uku daga asusun Gwamnatin Tarayya a tsawon shekara takwas da ya yi yana mulki, amma ya bar wa jihar bashin naira biliyan 500 da rashin biyan kuɗin wasu ayyuka na naira biliyan 300 bayan ya sauka.
Haka kuma, ƙungiyar ta zargi Mista Emmanuel da kasa yin bayani kan yadda aka kashe wasu maƙudan kuɗi har naira biliyan 700 kamar yadda aminiya ta ruwaito.
Leave a Reply