Hassan Turaki.
Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mandalari da ke Konduga a Jihar Borno, ta hallaka mutane biyu tare da jikkata wasu da dama.
Gobarar, ta tashi da ƙarfe 11:25 na safiyar Juma’a, 28 ga watan Fabrairu, 2025, ta bazu zuwa yankunan da ke da cunkoson jama’a, inda ta cinye matsugunan wucin gadi da kuma kayayyaki masu tarin yawa.
Sojojin da aka jibge a Konduga, sun kai ɗauki nan take bayan samun labarin tashin wutar tare da ha gwiwa da jami’an agaji da kuma al’ummar yankin domin shawo kan gobarar.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Borno, tare da haɗin gwiwar sojoji da hukumomin agaji, sunyi ƙoƙarin shawo kan lamarin.
Leave a Reply