Ashiru Gambo.
Professor Suwaiba Sa’id Ahmad Ta Raba Shinkafa Ga Masarautu Biyar Na Jihar Jigawa.
Ƙaramar ministan ilimi Prof. Suwaiba Sa’id Ahmad ta raba shinkafa ga dukkanin masarautun jihar Jigawa guda biyar, an fara rabon shinkafar ne a jiya Asabar in da aka fara da masarautun Kazaure, Gumel da kuma Haɗejia, yayin da aka kammala yau Lahadi da masarautun Ringim da kuma Dutse.
Rabon shinkafar ya gudana ne ta hannun hadimanta ga waɗannan masarautu masu daraja na jihar Jigawa guda biyar, wannan ƙoƙari da Prof. Suwaiba Sa’id tayi na da alaƙa da lokacin da yake tunkaro mu na watan Azumin Ramadan mai al-barka, muna fatan Allah ya sakawa wannan baiwar Allah da al-khairi.
Leave a Reply