JIGAWA: Mummunan hatsari ya lankwame rayuka …

Hassan Turaki.

Mutane huɗu sun rasa rayukansu, wasu 10 kuma sun samu raunuka bayan wata motar bas ƙirar Hummer ta kama da wuta a garin Gwaram dake Jihar Jigawa.

Kamar yadda jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandan jihar Jigawa SP Lawan shiisu Adam ya tabbatar cewa lamarin ya faru ne da ƙarfe hudu na yammacin ranar Asabar, a kusa da makarantar sakandaren gwamnati ta (Government Girls Unity Secondary School) da ke Gwaram.

Shiisu ya kara da cewa motar ta taso ne daga Ƙaramar Hukumar Zaki ta Jahar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi dake Ƙaramar Hukumar Gwaram.

Sanarwar ta bayyana cewa motar na ɗauke ne da fasinjoji 44, wanda suka haɗa da manya 25 da yara 19, wutar ta samo asali ne daga katifa da aka ɗaure a bayan motar, kusa da bututun fetur kuma tayi ta ci har takai ga taci galabar motar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *