Ashiru Gambo.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibril yayi rabon motoci 61 da babura 1,136 ga shugabannin jam’iyyar APC a jihar Kano.
GuaranteeNews ta ruwaito cewa an yi rabon ne da nufin karfafa ‘gwiwar ya’yan jam’iyyar APC da kuma saukaka gangamin goyon bayan jam’iyyar tun daga tushe a jihar kano.
Jibril ya ce za’a raba baburan ga shugabannin jam’iyyar na mazabu, yayin da motocin kuma za’a raba su ga shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi da na shiyya-shiyya.
Ya kuma bayyana shirin baiwa dalibai da suka kammala jami’a rancen kudi Naira miliyan 5 domin fara kananan sana’o’in dogaro da kai.
sanatan ya yaba wa matasa dake kokarin neman na kansu don
Leave a Reply