Ashiru Gambo.
Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) dake Ile-Ife, ta bayyana aniyarta na karrama Olabode Olawuyi, wani fasihin ma’aikaci mai kula da dabbobi da zaki ya kashe a gidan namun dajin jami’ar.
Registrar na jami’ar, Adetunji Bakare, ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin wani taron bita na yini guda domin tunawa da cikar shekara guda da rasuwar Olawuyi, wanda aka gudanar a Pit Theatre, Sashen Fasaha na Wasan Kwaikwayo, na Jami’ar ta OAU.
An shirya taron ne karkashin jagorancin Kungiyar Ma’aikatan Fasaha ta Jami’a (NAAT) da taken “Fahimtar Tsaron Ma’aikata a Wurin Aiki”.
Guarantee news ta rawaito cewa Olawuyi ya rasu ne a ranar 19 ga Fabrairu, 2024, yayin da yake kokarin ceton wani karamin abokin aikinsa da zaki ya kai wa hari lokacin ciyar da shi.
Registrar din jami’ar ya bayyana cewa taron ba wai domin murnar rasuwar Olawuyi ba ne, “amma domin girmama jarumtar sa.”
Mr. Bakare ya tabbatar da cewa jami’ar za ta dauki mataki na musamman domin tunawa da marigayi Olawuyi.
Leave a Reply