Hassan Turaki.
Majalisar Dattijan Najeriya ta daura laifin hatsaniya da ta faru a zauren ta kan sanata Natasha Uduaghan dake wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya.
Mai magana da yawun majalisar Yemi Adaramodu ya fada wa manema labarai cewa ya kamata Natasha ta san majalisa wuri ne na tattauna muhimman abubuwa.
A ranar Alhamis ce aka samu cece-kuce tsakanin sanatar da kuma shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio bayan an bukaci Natasha ta koma wata sabuwar kujerar zama da aka bata maimakon inda ta saba zama.
Mai tsawatarwa na majalisar, sanata Mohammed Munguno ya fada cewa dalilin da yasa aka ba ta sabuwar kujera shi ne na cike gurbin da wasu ‘yan majalisar biyu suka samar bayan ficewa daga wata jam’iyyar adawa zuwa ta APC mai mulki.
Amma kuma sanata Natasha taki yarda ta zauna a sabuwar kujerar da aka bata inda tayi amfani da doka mai lamba 10 da ta nuna an karya mata ‘yancin ta na kasancewa ‘yar majalisa.
Leave a Reply