Hassan Turaki.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya gargaɗi ƙasashe cewa Najeriya ba za ta yarda da rashin girmamawa daga kowace ƙasa ba.
Ya bayyana hakan ne bayan da Ƙasar Kanada ta hana wasu jami’an sojin Najeriya takardar izinin shiga ƙasar, duk da cewa an gayyace su don halartar wasannin Invictus a Vancouver.
Da yake jawabi a Hedikwatar Tsaro dake Abuja, bayan tarbar sojojin da suka halarci gasar, Musa ya nuna takaicin sa kan yadda ake nuna wa ‘yan Najeriya rashin adalci a wasu ƙasashe
A karshe, ya jinjina wa sojojin da suka wakilci Najeriya a gasar, inda ya tabbatar musu da cewa gwamnati ba za ta bari su wulaƙanta ba.
Leave a Reply