BOMB: Mutum bakwai sun rasa ransu a garin yani dake safana …

Hassan Turaki.

Wani jirgin sojin Najeriya ya jefa bom kan fararen hula inda ya kashe mutum bakwai a yankin Yani da ke Ƙaramar Hukumar Safana ta Jihar Katsina.

Mamatan sun hada da mutum shida ’yan gida ɗaya, kamar yadda wani shaida ya bayyana.

Hakan na zuwa ne bayan wasu jami’an tsaro da suka hada da ’yan sanda biyu da wani jami’in Rundunar Tsaron Al’umma na jihar (CWC) sun kwanta dama a yayin musayar wuta da ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar a ranar Asabar.

Jaridar Guarantee News ta rawaito cewa wani mazaunin Gundumar Zakka da ke Ƙaramar Hukumar, yankin da abin ya faru, ya bayyana cewa an yi arangamar ne bayan zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar ranar Asabar, inda ’yan bindiga suka shirya kai wa masu zaɓe hari a kauyen Zakka.

Bayan samun rahoton shirin harin ne jami’an tsaron suka je domin daƙile ’yan bindigar, inda a garin haka aka yi musayar wuta tsakanin bangarorin. Wani hafsan dan sanda da jami’in CWC sun rasu, daga bisani wani ɗan sanda da ya ji rauni a arangamar ya cika.

A cewarsa, “bayan nan ne wani jirgin soji ya zo, watakila domin kai wa jami’an tsaron ɗauki. A nan ne ya jefa bom a yankin Yani da ke ƙauyen Zakka, wanda ya halaka mutum shida ’yan gida ɗaya, ya kuma jikkata wata mata.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *