An bukaci majalissar tarayyar Africa da su saukaka tsarin Visa …

Hassan Turaki.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci ƙasashen duniya da su sauƙaƙa tsarin ba da biza ga kamfanonin Najeriya dake ƙoƙarin kafa masana’antu da kasuwanci a ƙetare.

Ministan yayi wannan kira ne a Addis Ababa, babban birnin Habasha, a ranar Lahadi yayin da yake wakiltar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a taron shugabannin ƙasashen Afirka karo na 38 da Majalisar Tarayyar Afirka (AU) ta shirya.

A yayin wata ganawa da shugabannin al’ummar Najeriya da ke Habasha, Idris ya jaddada cewa Najeriya na samar da kyakkyawan yanayi ga kamfanonin ƙasashen waje don su zuba jari a cikin ƙasar, don haka ya dace a samar da irin wannan dama ga ‘yan kasuwar Najeriya a ƙasashen waje.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *