NIJER: Kungiyoyin fararen hula a Nijar sunyi fatali da taron dawo da demokradiyya …

ibrahim Adamu Dutse.

Kungiyoyin fararen hula na kasar Nijar sun kaura cewa taron da aka shirya guda nar wa domin tsara yadda za a mayar da mulki ga farar hula bayan han barar da gwamnatin bazum.

Yayin da za a fara babban taron ƙasa a Jamhuriyar Nijar, domin tsara yadda za a mayar da mulki ga gwamnatin farar hula, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, wanda ya kifar da zababbiyar gwamnatin farar hula ta Mohammed Bazoum, kungiyoyin fararen hula sun kauracewa halartar taron.

Ana dai ganin kamar taron ba zai yi armashin da aka yi zato ba saboda yadda ƙungiyoyin fararen hula suka bayyana aniyarsu ta ƙauracewa taron.

Shugaban mulkin soja na kasar janar Abdourahmane Tchiani, wanda ya kira taron ya ce za ayi amfani da abin da aka tattauna ne wajen tsara abubuwan da gwamnati zata tattauna akai da kuma lokacin mika Mulki ga sabuwar gwamnati.

Tun bayan hambarar da da gwamnatin shugaba Bazoum a watan Yulin 2023, janar Tchiani ya yi alkwarin mayar da Mulki ga farar hula a cikin shekaru uku.

to amma shafe dogon lokaci ba tare da ganin an fara daukar kwararan matakai a kan mika mulkin ba, ya sanya an fara nuna shakku a kan tabbatuwar hakan.

Kazalika akwai masu sharhin da ke ganin cewa, duk da kiran gudanar da babban taron na kasa da shugaban mulkin sojin na Nijar ya yi, ba lallai su mika Mulki ga farar hula ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *