WUNTI ALKHAIR: Ku guji bada kuɗin rijistar tallafi …

Hassan Turaki.

An ja Hankalin gidauniyar Wunti Al-khair kan yadda wasu bata gari ke karban naira 200 ko abin da yafi haka da sunan rijistan tallafin shinkafa, kudi da sauran muhimman kayaki.

Yana da kyau alumma ta sani cewa gidauniyar Wunti Al-khair bata taba karbar ko sisin kobo ba a hanun Jama’a musamman masu bukatar tallafi kuma bata bada dama wa kowa yayi rigistar tallafi a madadin ta ba.

Dan haka, gidauniyar Wunti Al-khair ke nesanta kanta da wadannan Yan damfara kuma ana shawartar sauran jama’a, shugabannin al’umma da jami’an tsaro da su dauki matakin da ya dace a kan wadanan miyagun mutane.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *