Rundunar yan sandan jihar plateau ta cika hanu da masu safarar harsashi …

Hassan Turaki.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, ta kama wani matashi tare da wasu mutum uku kan zargin safarar harsasai daga Jos zuwa Abuja.

Matashin ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun biya shi Naira 50,000 domin ya karɓo harsasai daga Jos zuwa Abuja.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, yayin da yake holen waɗanda ake zargi, ya ce an kama su ne bayan samun rahoton sirri kan ayyukansu, da cewar rundunar na ci gaba da bincike, kuma da zarar an kammala, za a miƙa su zuwa kotu domin fuskantar hukunci.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *