RAMADAN: Gwamna bago yace zai karya farashin kayan abinci …

Hassan Turaki.

Gwamnatin jihar Neja ta kammala shirinta na zabge farashin kayan masarufi saboda zuwan watan azumin ramadan.

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ne ya sanar da hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar gidauniyar ‘Gates’ a fadar gidan gwamnati dake Minna.

Gwamna Bago yace ya ɗauki matakin ne domin sauƙaƙa wa al’umma a lokacin azumin watan Ramadan.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *