Hassan Turaki.
MAI MARTABA SARKIN DUTSE ALH. MUHAMMAD HAMIM NUHU SANUSI CFR ya ziyarci Fadar Mai Martaba Sarkin Jiwa dake Abuja Alh. Idris Musa bisa rasuwar Mahaifiyar sa.
Sarkin ya samu rakiyar MAI MARTABA SARKIN MORIKI ALH. BASHIR ISMA’IL AR. III dake Jihar Zamfara, da Mai Girma Sarkin Fadar Dutse Alh. Wada Alhaji Shugaban Ma’aikata na Fadar Mai Martaba Sarki kuma Ɗan Majalissar Sarki, da sauran ‘yan Rakiya.
A yayin ziyarar da yakai, Maimartaba Sarkin Dutse yayi jawabi me ratsa jiki dangane da mutuwa harma yayi addu’ar neman gafara gare ta.
Da yake nasa jawabin maimarta Sarkin Jiwa Alhaji Idris Musa yayi godiya da nuna farin cikin sa ga tawagar da yace tayi tafiya na tsawon lokaci har zuwa fadar sa dake abuja domin yi masa ta’aziyya, yayi addu’ar ALLAH ya mayar dasu gida lafiya.
Muna masu Addu’ar Allah ya jikanta da Rahama ya sa Aljannah Makoma.
Daga Fadar Mai Martaba Sarki.
Leave a Reply