SARKIN DUTSE: Maimartaba Sarkin Dutse ya ziyarci shehun Borno gabanin bikin bada …

Hassan Turaki.

MAI MARTABA SARKIN DUTSE ALH. MUHAMMAD HAMIM NUHU SUNUSI CFR, ya isa Ƙasar Maiduguri domin halartar Bikin Bayar da Sandar Girma ga Mai Martaba Shehun Bama ALH. DR. UMAR IBN KYARI UMAR AL-AMIN EL-KANEMI.

Ya fara da ziyartar Uban Ƙasa Shehun Borno wadda suka haɗu da Mai Martaba Sarkin Argungu, da Sarkin Kagara, kana daga bisani aka garzaya zuwa ƙasar Shehun Bama a inda aka gaisa a Fadar sa dake cikin garin Bama kafin Gobe a gudanar da biki.

Mai Martaba Sarki ya samu rakiyar MAI MARTABA SARKIN MORIKI ALH. BASHIR ISMA’IL AR. III dake Jihar Zamfara, da kuma Mai Girma Chiroman Dutse Sarkin Fada, Sarkin Gabas, Baura da kuma Majidaɗi, sai Fadawan Sarki da Dogarai.

Allah ya taimaki Sarki, Allah ya Ƙarawa Sarki lafiya, Allah yaci gaba da ɗaukaka Masarautun nahiyar mu baki ɗaya.


Nasir Ibrahim
Wazirin Tafarkin Dutse.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *