NIJER: Za’a koma mulkin farar hula a jamhuriyar Nijar …

Hassan Turaki.

Gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar, ta kafa kwamitin da zai gudanar da babban taro domin tsara dokoki kan tafiyar da ƙasa a lokacin mulkin su na rikon kwarya.

Ɗaya daga cikin manya-manyan abubuwa da ƴan ƙasar ke son su ji shi ne wa’adin da mulkin rikon kwaryar sojojin zai ɗauka.

“Mun tsara duk wanda za’a tura zuwa taron ya kasance wanda ya san matsalolin da suka shafi jihar da kuma zai iya cire kitse daga wuta,” a cewar Abdu Ɗan Naito, shugaban ƙungiyar farar hula na Kodaye a Katsinan Maraɗi.

Ya ce abin da ƴan ƙasar ke son gani daga wajen mambobin kwamitin shi ne a tattauna kan matsaloli da ƙasar ke ciki da kuma magance su ta yanda kowane ɗan ƙasa zai samu moriya.

Wasu daga cikin ƴan Jamhuriyar ta Najeriyar ɗin na fatan cewa waɗanda ke cikin kwamitin ba ƴan amshin shatan sojoji da ke mulki bane.

Taron muhawarar dai shi ne irinsa na farko da sojojin suka kira don ƙoƙarin ganin an koma mulkin dimokraɗiyya tun bayan hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *