Politics

AN KUMA: Ina sane da shirin kama Ni da zarar na shigo Nigeria kuma ba fashi zan shigo …

Hassan Turaki.

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El- Rufai ya ce ba zai yi gudun hijira ba duk da raɗe-raɗin da ake yi na cewa ana shirin kama shi tare da azabtar da shi.

El-Rufa’i ya faɗi haka ne a martanin da ya mayar a shafinsa na twitter bayan da wani mai amfani da shafin ya wallafa cewa ya samu bayanai masu ƙarfi da ke nuna ana shirin kama El-Rufa’i.

Tsohon gwamnan Kaduna ya ce ”Na daɗe ina jin waɗannan raɗe-raɗin kan kama ni da tsare ni da kuma azabtar da ni a wani ɗakin azabtarwa dake ofisihin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (wurin da ake zargin an azabtar ta Emefiele domin ya bar aiki a matsayin gwamnan CBN), tun watan Yulin 2024 lokacin da aka fara yaɗa rahoton majalisar dokokin jihar Kaduna” in ji shi.

Ya kuma ce an aika irin waɗannan sakonnin barazanar ta hanyar abokai da ƴan uwanshi da dama saboda ana so ya ji tsoro yayi gudun hijra da kanshi, sai dai El-Rufai yace ” ba zan yi hakan ba”.

Ya kara da cewa kafin ranar 20 ga watan Fabrairu zai dawo Najeriya, ya kuma ce ya dakatar da karatun da yake yi da kuma shirin koyon wasu harsuna zai dawo gida Najeriya, domin a cewarsa ba zai ci gaba da yin shiru ba.

El-Rufa’i ya kuma ce kamawa da tsarewa da kuma azabtar da abokan hamayya a siyasa ba sabon abu ba ne, ”ni kaina an kama ni kuma an kulle ni sau uku a baya saboda bayyana ra’ayi na kan gwamnatocin baya.” a cewarsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button