GWAMNA ABBA KABIR YUSUF YA RANTSAR DA SABON SAKATAREN GWAMNATIN JIHAR …

Ashiru Gambo.

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano a wani biki na musamman da aka gudanar a fadar Gwamnati.

Gwamnan ya jaddada cewa sabon Sakataren Gwamnati zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da aiwatar da manufofin gwamnati domin ci gaban jihar Kano. Ya kuma bukaci shi da ya yi aiki tukuru tare da sadaukar da kansa wajen inganta harkokin shugabanci da kyautata jin dadin al’umma.

Sabon Sakataren Gwamnati, a nasa bangaren, ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa amincewa da shi, tare da alkawarta yin aiki tukuru don tallafa wa gwamnatin jihar wajen cimma nasarori.

Wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnatin Kano na inganta harkokin mulki da tabbatar da ci gaba a jihar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *