Hassan Turaki.
Wata gobarar iskar gas ta tashi a Sabon Wuse, ƙaramar hukumar Tafa a Jihar Neja, a ranar Lahadi, kusan wata guda bayan fashewar tankar mai a Dikko Junction, kan titin Abuja-Kaduna.
Sabon Wuse na da tazarar kilomita uku daga Dikko Junction, inda haɗarin tankar mai ya faru a baya. Wannan fashewar ta faru ne yayin da ake sauke lodin gas.
Shugaban hukumar kula da afkuwar bala’o’i ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da afkuwar lamarin, da bayyana cewa babu asarar rai, amma gobarar ta lalata motocin da shaguna da ke kusa da wurin.
Leave a Reply