KANO: Hukumar tace fina-finai ta dakatar da wani “Film” na badala …

Hassan Turaki.

Film din mai suna “Zarmalulu” ana zarginsa da rashin ma’ana tare da kama da wani suna na badala, a saboda da haka Hukumar ta dakatar da shi tare da kira ga dukkannin wanda suka fito a cikin sa dasu bayyana a gaban kwamatin da Hukumar ta kafa wanda kin yin hakan ka iya jawowa mutum fushin Hukumar.

Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, yace hukumar na da hurumin kan dakatar da dukkannin wani film da bata gamsu da yadda aka shirya shi ba tare da laddaftar da duk wani da ta samu da yin abinda bai kamata a cikin kowanne film ba ko kuma a wajen film din matsawar dan Masana’antar kannywood ne.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *