HADEJIA: Gawuna ya halarci naɗin sarautar Mohammed Babandede a matsayin sabon Magajin Rafin Haɗeja…

Ashiru Gambo
Mai girma tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, wanda yayi wa jam’iyyar APC Takarar Gwamna kuma Shugaban Hukumar Gudanarwa na Jami’ar Bayero dake Kano, haka zalika sabon Shugaban Hukumar Gudanarwa na bankin Federal Mortgage Bank of Nigeria, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya jagoranci tawaga zuwa fadar garin Haɗejar jihar Jigawa don shaida naɗin sarautar aminin sa Alh. Mohammed Babandede (Area Controller of Custom) amatsayin Magajin Rafin Haɗeja kuma Ɗan Majalisar Sarki, wanda Mai Martaba Sarkin Haɗeja kuma Shugaban Majalisar Sarakunan jihar Jigawa, Alh. Adamu Abubakar Maje CON. yayi masa, wanda aka gudanar a Fadar ta Mai Martaba sarkin Hadejan, dake cikin jihar ta Jigawa.
Shi sabon Magajin Rafin Haɗejan Alh. Mohammed Babandede (Area Controller of Custom) ya kasance ɗan uwa ne ga tsohon shugaban hukumar kulqada shige da fice ta ƙasa (Controller General of Immigration Rtd) Alh. Muhammad Babandede OFR, OCM.
Dr. Nasiru Gawunan ya taya sa murna matuƙa da addu’ar fatan Allah Ya riƙa masa.