Taƙaitaccen Tarihin Rayuwar Tsohon Gwamnan Soja na Jihar Katsina Marigayi Isah Kachako …

Saleh Hussaini Takai.

An haifi marigayi Sanata Col. Isa Kachako mai ritaya a ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1940 a garin Kachako da ke yankin ƙaramar hukumar takai a yanzu.

Ya fara karatun mahammadiya a gaban mahaifin sa daga bisani ya shiga makarantar Firamare a shekarar 1950 zuwa 1953 a garin Durbunde.

A shekarar 1954 zuwa 1956 marigayi Sanata Col Isa Kachako ya halarci makarantar middle dake birnin kudu ta jihar Jigawa a yanzu.

A Shekarar 1957 ya shiga makarantar horas da malaman makaranta ta Wudil teachers College inda ya samu tsawon shekaru biyu kuma bayan ya kamallla a shekarar 1958 ya zama malamin makarantar firamare.

Marigayi Sanata Col. Isa Kachako an bashi matsayin shugaban makaranta wato headmaster a garin kila a shekarar 1961 har zuwa 1962 daga bisani aka canja masa wajen aiki zuwa makarantar firamare ta sara a dai matsayin headmaster daga shekarar 1962 zuwa 1965 dukka a karamar hukumar gwaram dake jihar Jigawa a halin yanzu.

A shekarar 1966 ya tafi ƙarin karatu zuwa babbar kwalejin horas da malaman makaranta ta Bichi inda ya samu shedar koyarwa ta grade II inda aka mayar dashi matsayin headmaster a babbar makarantar firamare ta garin wurno.

Marigayi Sanata Col. Isa Kachako ya aje aikin Koyarwa inda a shekarar 1968 ya tafi kwalejin koyar da tukin jirgin sama ta rundunar sojin sama ta ƙasa.

Daga bisani ya tafi karɓar horon aikin sojin kasa a Nigerian defence academy emergency course 5 Wanda ya bashi damar canjawa daga sojin sama zuwa sojin ƙasa. Daga shekarar 1968 zuwa 1971 inda ya fito a matsayin cikakken Kanal. Na sojin kasa na Najeriya.

A shekara ta 1971 marigayi Sanata Col. Isa Kachako ya zama Fulatun Kwamandan kuma na biyu a bataliya ta 133 dake owo sai kuma bataliya ta 186 dake ibadan har zuwa shekarar 1974.

A shekarar 1974 zuwa 1977 marigayi Sanata Col. Isa Kachako ya zama mai bayar da horo a Nigeria defence academy dake Kaduna.

Col. Isa Kachako ya zama wakilin Najeriya a kasar India tsawon shekaru 2. Bayan dawowarsa gida Najeriya ne marigayi Sanata Col Isa Kachako ya zama mataimakin shugaban bataliya ta 15 dake Yola jihar Adamawa daga 1981 zuwa 1983 har ya zama shugaban bataliyar.

Ya zama shugaban ma’aikata a grade II division daga nan kuma aka nada shi kwamandan bataliya ta 26 dake elele a fatakwal sai kuma ya zama kwamandan bataliya ta 82 dake Katsina daga nan ya zama darakta na Combat training tradoc dake mina ta jihar Neja.

A shekarar 1987 marigayi Sanata Col Isa Kachako ya zama gwamnan Katsina na riko na mulkin soji kyakkyawan jagoranci da ya yi a Katsina a wancan lokaci yasa Sarkin Katsina ya aura masa diyyar sa wadda tana cikin matan da zasu yi masa takaba.

Bayan ritayar sa daga aikin soji marigayi Sanata Col Isa Kachako sai ya shiga harkokin wasanni domin masoyi ne ga harkokin wasanni inda har ya zama shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano daga shekarar 1990 zuwa 1991, ya kuma zama shugaba na farko na Nigerian Milo marathon, daga nan ya zama chairman kaduna referees association, ya Kuma zama chairman Niger state football association, haka ya zama national chairman sports festival. Kuma Member a hukumar wasanni ta duniya FIFA, sai kuma member a Kaduna polo club, ya zama memba a new delhi Indian polo club, chairman Nigeria army polo club, ya rike muƙamin shugaban kungiyoyin wasanni daban daban. Kuma yana daya daga cikin mutane mafiya shahara a wasan ƙwallon doki a Afrika.

Marigayi Sanata Col Isa Kachako daga nan ya shiga harkokin siyasa inda ya zama sanata Kano ta kudu a jam’iyyar NRC a shekarar 1992 zuwa 1993. Ya taba zama shugaban matasa na kasa haka shine daraktan tsaro da tsare-tsaren takarar marigayi Yar’adua a shekarar 2007. Ya yi shugaban jam’iyyar ANPP ya kuma rike muƙamai da dama a jam’iyyar haka ya shiga jam’iyyar PDP inda nan ma ya rike mukamai masu yawa a jam’iyyar.

Sanata isa Kachako shine ya wakilci jihar Kano a taron gyara kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 kuma yana daya daga cikin mutanen da suka shige gaba aka kirkiri jihar Jigawa ya kuma taba zama mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa janar sani abacha.

Marigayi Sanata Col Isa Kachako shine Turakin Kachako Wanda a lokacin rayuwar sa ya karbi lambobin yabo ciki harda Wadda kasar Amurka ta bashi da wanda ya samu daga wasu ƙasashe dana gida masu tarin yawa.

Akwai ɗaliban da ya koyar lokacin yana malamin makaranta wanda suka yi fice a fannoni daban daban ciki harda Dan Adalan Kano Alh isiyaku tofa.

Mutun ne wanda ya rike al’umma da dama ya kula da karatun su da dawainiyar rayuwar ba tare da yasan su ko asalin su ba, kullum gidan sa ciyar da al’umma ake yi babu kakkautawa mutum mai jinƙai da tausayi da taimako wanda duk abun da ya samu rabarwa al’umma ya ke kullum yana faɗin bai yi amfani da kowane irin mukami da ya samu ba ya saci dukiyar al’umma

Marigayi Sanata Col Isa Kachako Ya rasu ya bar mata uku da ya’ya bakwai da jikoki masu matansa sun haɗa da Hajiya Asabe da Hajiya Halima da kuma
Hajiya Aisha sai ‘ya ‘yan sa da suka haɗar da Yusuf isa Kachako wanda ma’aikaci ne a hukumar raya Yankin arewa maso yamma da A’isha Isa Kachako da Hadiza Isa Kachako da Rahina Isa Kachako Eng. Ahmad Isa Kachako da Nafisa Isa Kachako da Abba Isa Kachako sai jikoki masu yawa.

Da fatan Allah ya jikan Turakin Kachako Sanata Col Isa Kachako ya sa aljanna makoma

Rubutawa ✍️
Hasheem Salihu Kachako


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *