Musa iliyasu Kwankwaso ya bukaci Ribadu da ya yi …

Ibrahim A. makama.

Wani jigo a jam’iyyar (APC) a Jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya shawarci Mai Ba shugaban kasa Shawara kan sha’anin Tsaro(NSA), Malam Nuhu Ribadu, da sauran manyan jami’an gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da su ci gaba da mayar da hankali kan aikinsu duk da sukar da ‘yan adawa ke yi musu.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano a ranar Juma’a, Kwankwaso ya yabawa kokarin Ribadu wajen inganta tsaron kasa tare da bukatar ya ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da aikinsa.

A cewarsa “Ribadu ya ci gaba da mayar da hankali wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Sauran jami’an gwamnatin Tinubu ma su mai da hankali kan aikinsu ba tare da damuwa da maganganun ‘yan adawa ba.

Kwankwaso ya jinjinawa nasarorin Ribadu a yaki da rashin tsaro, yana mai cewa yankuna da suka kasance da hadari a baya sun zama mafi aminci, inda aka kawar da dama daga cikin ‘yan ta’adda da kuma Boko Haram, yayin da wasu suka mika wuya.

Ya zargi wasu ‘yan adawa, ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, da rashin jin dadi kan nasarorin Ribadu.

“Ba sa farin ciki saboda NSA da sauran manyan jami’ai suna ba wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu alfahari ta hanyar kyakkyawan aikinsu.

Dangane da siyasar Kano, Kwankwaso ya bayyana cewa APC tana kara samun karfi, yana mai yin nuni da sauya sheka da wasu tsofaffin kwamishinoni na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) suka yi zuwa APC.

“Kwanan nan, wasu tsofaffin kwamishinonin NNPP sun koma APC a gaban Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin. Wannan ci gaban ya tada hankalin Dakta Rabi’u Kwankwaso,” in ji shi.

Kwankwaso ya bayyana kwarin gwiwa kan makomar APC a Kano, yana mai alkawarin ci gaba da jawo mambobin NNPP domin tabbatar da jam’iyyar ta karbe mulki a jihar nan da 2027.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *