DUTSE: Wani yaro ya samu kyautar doki daga mai martaba sarkin Dutse …

Hassan Turaki.

Cikin ikon Allah da yammacin wannan rana MAI MARTABA SARKIN DUTSE ALH. MUHAMMAD HAMIM NUHU SANUSI CFR ya halarci wajen Rufe Gasar Tseren Sukuwa ta Doki wacce Ƙungiyar Dutse Emirate Horse Racing Club suka shirya domin Cikar Shekara biyu na Mai Martaba Sarkin Dutse bisa Gadon Sarauta.

An gudanar da Gasar ne a Filin Idi dake Babban Birnin Jiha wato Dutse, Jihar Jigawa.

Wadda Sama’ila (Sarki Ma’il) Allah ya bashi nasara ya zama zakaran Gwajin Dafi yazo na Ɗaya ya kuma samu kyautar Doki sai sauran masu biye masa suka samu ribar kuɗaɗe.

Taron ya samu Halartar Mai Girma Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Dutse, ‘yan Majalissar Sarki da sauran Manyan Mutane.

Allah ya Taimaki Sarki, Allah yaja zamanin Sarki, Sarki kake baƙon Dole. Sarkin Haɗaɗɗiyar Daular Dutse.


Nasir Ibrahim SNITP
Wazirin Tafarkin Dutse
Fadar Mai Martaba Sarki.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *