BINCIKE; An gano mutum dubu shida da akayi wa katin dan kasa ta hanyar bogi …

Guarantee Media.

Nijeriya ta gano ‘yan Nijar 6,000 da aka yi wa rajistar samun lambar NIN da ke nuna asalin ‘yan kasa

Garantee Media ta rawaito cewa ministan harkokin cikin gida na Nijeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar da hakan, inda yace gwamnatin tarayya ta umarci da a gaggauta kwace wadannan lambobi na NIN da aka ba ‘yan Nijar. Matakin da Ministan yace tuni an aiwatar da shi, an goge su daga manhajar ma’aikatar.

ya kara da cewa hukumomi za suyi binciken kokof domin zakulowa da kuma hukunta duk wadan da abun ya shafa.

wannan dai kalubale ne ga ma’aikatar katin dan kasa a Najeriya wato (NIMC) da tayi duk me yiwuwa ganin ta toshe irin wadannan hanyoyi da ake bi ake tafka magudin fitar da katin ta hanyar da bata dace ba


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *