Hassan Turaki.
Matasa Sun Nemi Injiniya Ayuba Dauda Katagum Ya Shiga Jam’iyyar PDP Don Haɗa Kai Da Taimaka Wa Ci Gaban Jihar Bauchi.
Ƙungiyar matasa a jihar Bauchi, Patriotic PDP Youths Forum ta yi kira ga Injiniya Ayuba Dauda Katagum, shahararren ɗan kasuwa, kuma shugaban Doxxie Global Solution Limited, da ya shiga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) domin mara wa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, baya.
Ƙungiyar ta bayyana cewa shiga PDP da Injiniya Katagum zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi, tare da bai wa matasa dama su haɗa kai don ci gaba da inganta jihar Bauchi.
Injiniya Katagum, wanda a baya ya nemi takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya taka rawar gani wajen cigaban al’umma musamman a fannonin ilimi da taimakon matasa.
Daya daga cikin manyan gudunmuwarsa shi ne kafa cibiyar koyon fasahar zamani kyauta (ICT Center) a Karamar Hukumar Zaki. Wannan cibiya na da nufin ba da horo kan ilimin kwamfuta ga matasa da sauran jama’a, Bugu da ƙari, Injiniya Katagum ya samar da rijiyoyin burtsatse don jama’a, ya bayar da tallafin karatu ga matasa masu hazaka, tare da goyon bayan shigar matasa cikin mulki. Waɗannan abubuwa sun nuna irin jajircewarsa wajen bunƙasa rayuwar matasa da ci gaban jihar.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa shigowar Injiniya Katagum cikin PDP zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da “Bauchi Sai Matashi Project 2027,” wanda ake ganin zai buɗe sabon babi a ci gaban jihar. Ƙungiyar ta jinjina wa Gwamna Bala Mohammed saboda irin yadda yake bai wa matasa dama a gwamnatinsa, lamarin da ke nuna cewa gwamnatinsa za ta kasance abokiyar tafiya da burin Injiniya Katagum.
A matsayinsa na gogaggen ɗan kasuwa mai alaƙa da al’umma, tasirin Injiniya Katagum da ƙwarewarsa za su kasance manyan ginshiƙai ga PDP wajen tabbatar da ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen raya jihar da cika burin matasa a Bauchi.
A ƙarshe, ƙungiyar Bauchi Patriotic PDP Youths Forum ta buƙaci Injiniya Ayuba Dauda Katagum da ya haɗa kai da PDP da Gwamna Bala Mohammed, domin tabbatar da cewa matasan Bauchi ba kawai ana damawa da su a harkokin mulki ba, har ma suna taka muhimmiyar rawa wajen gina makomar jihar. Lokaci ya yi da matasa za su haɗa kai su yi aiki tare domin samun Bauchi mafi inganci.
Leave a Reply