Hassan Turaki.
Cikin ziyarar tasu Mamallakin Jami’ar ya yiwa Mai Martaba Sarki bayanin yadda wannan Jami’a ta kasance tun daga lokacin da suka fara shawarwarin kafa ta har kawo yanzu wadda take da Ɗalibai kusan Dubu Biyu (2,000).
Haka zalika, ya bayyanawa Mai Martaba Sarki shirin da sukayi na bawa Marigayi wato Mai Martaba Sarki Alh. Dr. Nuhu Muhammad Sanusi CON Allah ya jiƙansa muƙamin Shugaban wannan Jami’a wato (Chancellor) wadda kafin sa Mai Martaba Sarkin Kano na (15) ne Shugaban wadda wa’adinsa ya cika na shekara biyu har sau biyu akan wannan kujera shi ne suka ga dacewa su kawo wannan kujera ya zuwa ga Mai Martaba Sarkin Dutse Alh. Muhammad Hamim Nuhu Sanusi CFR.
Ya ƙara da cewa dalilin bashi wannan matsayi shi ne, bawai iya Maƙotaka da aka haɗa tsakanin Dutse da Sumaila ba sun duba yadda wannan Masarauta tayi fice wajen Hidimtawa Addinin Musulunci musanman ayyukan Zakkah da Waqafi. Kana sun nemi Mai Martaba ya karbi wannan Matsayi bawai don su ba sai don ayyukan Alheri da wannan gida na Masarautar Dutse yake yi. Kana suka danƙa masa Takarda ta tabbatar masa da wannan matsayi.
A nasa jawabin, Mai Martaba Sarki ya yaba wa Sanatan Kano ta Kudu da ma Shuwagabannin wannan Jami’a da suka ga ya cancanci wannan Karamci da Matsayi. Mai Martaba ya yaba musu kwarai da gaske wadda yace baiyi mamakin wannan matsayi da suka bashi ba duba da burin da Marigayi yaci akan wannan Makaranta wadda yake so ta kasance kamar jami’ar Masar wadda Allah baiyi zai shaida wannan matsayi ba amma gashi sun shaida.
A ƙarshe ya musu fatan alheri da fatan Nasara da kuma ganin suna gudanar da ayyukan Zakkah a Jihar Kano wadda yace Kano Uwa ce kuma ma bada Mama.
ya kara da cewa ba ƙaramin alheri za’a samu ba a jihar Kano na harkar Zakkah.
Tawagar ta samu tarba a wajen ‘yan Majalissar Sarki daga cikin su akwai Mai Girma Galadiman Dutse, Wamban Dutse, Madakin Dutse, Da sauran yan majalissar sarki
Allah ya taimaki Sarki, Allah yaja zamanin Adalin Sarki, Allah ya bar Sarki da Masoyan sa.
Nasir Ibrahim sMNITP
Wazirin Tafarkin Dutse.
Leave a Reply