Ibrahim Adamu Dutse.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sauke shugabar Jami’ar Abuja da aka sauyawa suna zuwa Jami’ar Yakubu Gowon, wato Farfesa Aisha Sani Maikudi, tare da rusa Majalisar gudanarwarta.
Sanarwar da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya gabatar, tace daga yanzu Sanata Lanre Tejuoso dake shugabancin majalisar gudanarwar Jami’ar Koyon aikin noma dake Makurdi shi ne sabon shugaban gudanarwar Jami’ar Yakubu Gowon, yayin da Farfesa Lar Patricia Manko za ta zama shugabar Jami’ar na riko na watanni 6, amma kuma ba za ta shiga takarar masu neman mukamin ba idan wa’adin ta ya kare.
Onanuga ya kuma kara da cewa shugaba Tinubu ya tube shugaban riko na Jami’ar Nsukka, Frafesa Polycarp Emeka Chigbu gabanin kkarewar wa’adinsa na ranar 14 ga wannan watan na Fabarairu, tare da nada Farfesa Oguejiofu T. Ujam a zaman shugaban riko na watanni 6.
Leave a Reply