Ko Barcelona Za Ta Iya Sake Zazzagawa Valencia Ƙwallaye 7 Yau?.

Ibrahim Adamu Dutse.

Biyo bayan nasarar da suka yi akan Alavés a ƙarshen mako, Barcelona za ta dawo taka leda a yau Alhamis don ƙarawa da Valencia a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Copa del Rey a filin wasa na Estádio de Mestalla dake Valencia.

Barcelona na cigaba da jan zarenta a wannan shekarar ta 2025, inda ta buga wasanni da dama ba tare da tayi rashin nasara ba tun bayan shigowar sabuwar shekara, kuma daya daga cikin mafi kyawun sakamakon da ta samu ya zuwa yanzu a bana shi ne wanda ta doke Valencia da ci 7-1 kwanaki 10 da suka gabata.

To amma a wannan karo akwai yiwuwar al’amura su sauya, ba kamar a wasan da ya gabata tsakanin ƙungiyoyin biyu ba, a wannan lokacin ba lallai Valencia ta iya kyale yaran na Flick su shakata a filin wasa na Mestalla kamar yadda suka yi a Luis Companys ba. Real Madrid ta doke Leganes da ci 2-3 domin samun damar zuwa matakin na kusa da na ƙarshe.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *