Ashiru Gambo.
Shugaban karamar hukumar Tarauni Alh Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure, ya jagoranci kaddamar da shirin duba lafiyar jama’a kyauta tare da bayar da magunguna ga sama da mutane 2,000 a asibitin Babbangiji Dake yankin karamar hukumar Tarauni.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na karamar hukumar Tarauni yafitar yace shugaban karamar hukumar Tarauni Alh Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure bayyana shirin da cewa yana daga cikin manyan ayyukan da ya aiwatar domin bikin cikarsa kwanaki 100 akan kujerar shugabancin karamar hukumar Tarauni.
A yayin kaddamar da shirin, wanda aka gudanar a asibitin Babbangiji da kuma sauran cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban a yankin Shugaban karamar hukumar ya Godiya Gwamna Abba Kabir Yusif da kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano, Alh. Tajo Othman Zaura bisa yadda suke basu wajan gudanar da aiyyukan raya kasa a fadin yankin karamar hukumar Tarauni.
Leave a Reply