Ibrahim Adamu Dutse.
Masarautar Gidan Igwai ta dakatar da Usman Umar wanda akafi Sani da (Soja Boy) daga sarautar Yariman Gidan Igwai sabo da zargin yada bâḍalâ
Takardar Sanarwar ta bayyana wasu abubuwa da masarautar tayi nazari ta dakatar da shi daga sarautar Yariman Gidan Igwai.
An dai samu bidiyon sa yana aikata abubuwan da suka sabawa addini, al’ada da dabi’un mutanen Gidan Igwai.
Bisa wannan dalili ne masarautar ta yanke hukuncin dakatarwa tare da tsige shi daga sarautarsa.
Hakazalika Sanarwar ta bayyana irin yadda Al’ummar yankin su yi tir da wannan dabi’a kuma sun nesanta kansu daga wannan abu mara kyau. Da tsohon basaraken yake aikatawa a wakokinsa.
Daga karshe masarautar tayi nasiha ga tsohon basaraken akan yaji tsoron Allah ya rungumi dabi’u irin na karantarwar addinin Musulunci.
Kamar yadda sanarwa mai dauke da saka hannun Alhaji Abubakar Marafa daga Ofishin Marafa Sarkin Adar, Gidan Igwai ta fitar.
Leave a Reply