NLC BAUCHI: Kungiyar kwadago a Nigeria reshen jihar Bauchi ta bayyana aniyar shiga yajin aiki …

Hassan Turaki.

Shugaban kungiyar NLC reshen jihar Bauchi Comrade Shuaibu Dauda ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa da aka gudanar a hedikwatar kungiyar ta NLC da ke Bauchi

Ya ce makasudin yajin aikin shi ne su bayyana kokensu game da karin kudin ƙira dana Data da hukumar sadarwa ta Nigeria ta yi.

Comrade Dauda Maidara Shuaibu ya bukaci daukacin kungiyoyin kwadago na jihar da su hada kan mambobinsu domin shiga yajin aikin.

Kungiyar NLC ta taka rawar gani wajen bayar da shawarwarin kare hakkin ma’aikata da kuma nuna adawa da manufofin da ke yin illa ga ma’aikata.

Kungiyar NLC ta kasa ta umurci reshen kungiyar na jihar Bauchi da ta dauki wannan mataki, wanda hakan ke nuni da matsayar kungiyar kan karin kudin harajin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *