KADUNA: Gwamna uba sani ya ƙaryata rade-radin da ake yi tsakanin sa da …

Hassan Turaki.

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, ya ce babu wata matsala tsakaninsa da magabacinsa Malam Nasir El-Rufai.

Uba sani ya ce babu kamshin gaskiya a maganganun da ke yawa cewa shi da tsohon gwamnan El-Rufai suna zaman doya da manja.

Ya bayyana haka ne a yayin hirar da kafar tala bijin ta TVC ta yi da shi a ranar Litinin, inda ya ce “alakarmu tana nan yadda ta ke, babu wata matsala, kamar yadda ake rade-radi.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *