“Ba ku da ikon ba da umarnin tsige ni” – Tinubu ya shaidawa kotu …

Ibrahim A makama

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta yi watsi da ƙarar da ke neman tilasta Majalisar Ƙasa ta fara shirin tsige shi daga mukaminsa bisa zargin take haƙƙin ‘yan ƙasa.

Wannan ƙara, mai lamba FHC/ABJ/CS/1334/2024, wani lauya mai suna Olukoya Ogungbeje ne ya shigar da ita a gaban kotu.

A cikin ƙarar, wanda ya haɗa da Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN, a matsayin wanda ake ƙara na biyu, mai shigar da ƙarar yana neman abubuwa guda shida daga kotu.

Ya bukaci kotu da ta ayyana cewa hana zanga-zangar lumana da gwamnatin Tinubu ke yi laifi ne da ya dace a tsige shi.

Misali, mai shigar da ƙarar ya zargi gwamnati da amfani da karfi wajen murƙushe masu zanga-zanga a tsakanin 1 zuwa 10 ga Agusta, 2024, a fadin ƙasa, lamarin da ya ce saba doka ne kuma hujja ce ta tsige shugaban ƙasa daga mukaminsa.

Ya kuma jaddada cewa sashe na 143 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi wa gyara) ya bai wa Majalisar Ƙasa damar ɗaukar matakin tsige shugaban ƙasa idan aka samu sabawa doka.

Sai dai a cikin wata ƙara ta ƙi amincewa da shari’ar da suka shigar da Shugaba Tinubu da Antoni Janar na Tarayya sun kalubalanci hurumin mai shigar da ƙarar wajen gabatar da ita.

Sun bukaci kotu da ta yi watsi da ƙarar, suna masu cewa babu wani dalili mai ma’ana da zai sa kotu ta amince da buƙatarsa.

Ta hanyar tawagar lauyoyinsu, ƙarƙashin jagorancin Sanusi Musa, SAN, Shugaba Tinubu da AGF sun kalubalanci ikon kotun wajen sauraron shari’ar.

Baya ga haka, waɗanda ake ƙara sun nemi kotu da ta ƙwace shari’ar gaba ɗaya, domin an shigar da ita ne ba bisa ka’ida ba kuma ta hanyar da ba ta dace ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *