KANO PILLARS: An samu sauyi a kungiyar kwallon kafa ta Kano pillars

Hassan Turaki.


Hukumar gudanarwar Kano Pillars ta dakatar da mai horasda kungiyar Usman Abdallah na tsahon makwanni 3.

Dakatarwar ta biyo bayan rashin tabuka abin a zo a gani a baya bayan nan, da kuma harzika magoya bayan kungiyar, bayan tashi daga wasan da Kano Pillars din ta buga chanjaras da Bayelsa United a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.

Sanarwar da Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Alhaji Ali na yara Mai samba ya sanya wa hanu ta ce, mataimakin mai horaswa na kungiyar Ahmad Garba Yaro-Yaro ne zai ci gaba da jan ragamar kungiyar kafin kwamitin bincike da hukumar gudanarwar na Kano pillars din ta kafa ya bayar da rahotan sa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *